RA'AYI: Yadda wasu ke yaɗa ƙarerayi don ɓatawa Sanata Shehu Buba suna
Daga: Mustapha Abubakar
A matsayina na ma'abocin hulɗa da kafafen sadarwar zamani, kuma manazarci kan harkokin siyasa da zamantakewar al'umma, fiye da tsawon shekaru goma, ina so na yi sharhi kan gudunmawar da Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar Ƙasa, Sanata Shehu Buba Umar yake bayarwa a wakilcin da yake yi wa al'ummar sa.
A wannan zamani da muke ciki, inda ake siyasantar da duk wani al'amari na jama'a a Najeriya, yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da cewa maganganun da ake yadawa, kan wasu muhimman mutane gaskiya ne, ba yaudara ba. Musamman ma ga al’ummar Jihar Bauchi, waɗanda suka cancanci samun ingantaccen bayani game da wakilinsu.
Ficen da Sanata Shehu Buba, ya yi ya zo ne bayan da ya yi takarar, kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayyaa mazaɓar Toro, har sau biyu a shekara ta 2015 da shekara ta 2019. Duk da kasancewar bai samu nasara ba, a dukka zaɓuɓɓuka biyun, amma farin jininsa ya cigaba da ƙaruwa, wanda hakan ya sa aka naɗa shi, shugaban riko na Ƙaramar Hukumar Toro.
Jajircewar Sanata Shehu Buba, na tallafa wa mabuƙata ya zama abin koyi, da yabawa ga al'umma da dama. Ƙoƙarin da ya yi na taimakon jama’a ya sa mutane da yawa suke ƙaunarsa, musamman waɗanda suke kallon sa a matsayin gwarzon marasa galihu. Sunansa na shugaba, mai kulawa da tausayi ya ƙara ƙarfi.
Abu ne mai sauƙi Shehu Buba ya samu takarar Sanata na jam’iyyar APC, duk da cewa a lokacin ne, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Naɗa Sanata Shehu Buba, a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa, mai kula da harkokin tsaro da leƙen asiri, ya nuna ƙwazo da jajircewarsa, wajen yi wa gwamnati hidima. Wannan Kwamitin mai karfi, an keɓe shi ne kawai ga ýan majalisa mafiya ƙwazo da amintattun ma’aikatan gwamnati a Majalisar Dattawa.
Hanyar da aka fi amfani da ita wajen shawo kan matsalolin tsaro ita ce ta ƙarfin soja. Amma duk da haka, akwai hanyoyin tattaunawa da diflomasiyya, su ma suna da muhimmanci wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ƙasashe da yawa, ciki har da kasashen da suka cigaba, kamar Amurka, ana amfani da hanyoyin ƙarfin soja da kuma hanyoyin tattaunawa don magance matsalolin tsaro.
A Amurka, ana amfani da hanyar ƙarfin soja wajen yaƙar ta'addanci. Haka kuma ana amfani da hanyoyin tattaunawa da haɗin gwiwar al'umma, don hana tsattsauran ra'ayi da haɓaka haɗin kan zamantakewa. Shirin wayar da kan jama'a na Hukumar Tsaro ta FBI da ke Amurka, yana hulɗa tare da al'ummomin gida, don gina amana da hana tashin hankali.
A ƙasashe irin su Somalia, an yi amfani da ƙarfin soja wajen yaƙar mayaƙan al-Shabaab, yayin da aka yi amfani da ƙoƙarin tattaunawa da sulhu, wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. A Najeriya ma, an yi amfani da ƙarfin soja wajen yaƙar Boko Haram, yayin da ake amfani da shirye-shiryen yin afuwa da tattaunawa, wajen gyarawa tare da mayar da tsoffin 'yan tada ƙayar baya.
Yin amfani da ƙarfin soja da hanyoyin tattaunawa kan samar da tsaro, bai taƙaita ga waɗannan ƙasashe kawai ba. Ƙasashe da dama, na bin tsarin tsaro da ya dace, ganin cewa ƙarfin soja kaɗai, bai isa a samu zaman lafiya, mai ɗorewa ba.
Masu suka, ya kamata su karkatar da hankalinsu, zuwa ga magance matsalolin ƙasa kamar rashin tsaro, talauci, da rashin aikin yi. Maimakon su mayar da hankali kan suka, za su iya ba da tasu gudummawar, wajen tattaunawa mai ma'ana kan yadda za a inganta tattalin arziƙin Nijeriya da tsaro. Ta yin haka za su kasance suna goyon bayan, ƙoƙarin shugabanni irin su Sanata Shehu Buba Umar da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, waɗanda suke aiki tuƙuru, domin samar da zaman lafiya da cigaba.
Matsalar tsaro a Najeriya, a halin yanzu na bukatar a bi matakai daban-daban, kuma Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Sanata Shehu Buba Umar, suna fafutukar ganin an samar da zaman lafiya, ba tare da tashin hankali ba. Sanata Buba ya ba da shawarar tattaunawa, sasantawa, da sabunta tattalin arziƙi, yana mai nuni da shaidar duniya cewa, tattaunawar ta yi nasara a sama da kashi 90% na lamuran.
Gamayyar Kungiyoyin fararen hula ta Ƙasa (NCSCN) ta yabawa Ribadu da Buba, kan ƙoƙarin da suke yi, inda suka haɗa da dabarun yaƙi da rashin tsaro. Wannan tsarin ya taimaka wajen rage tashe-tashen hankula a faɗin ƙasar nan.
Wajibi ne jama’a su tantance bayanan da suke amfani da su, domin jin daɗin ƙoƙarin da Malam Nuhu Ribadu da Sanata Shehu Buba Umar suke yi na samar da zaman lafiya. Yunƙurin su na tunkarar tsare-tsaren gwamnati ya bayyana a cikin ayyukansu. Ta hanyar haɓaka haɗin kai da haɗin gwiwa, 'yan Nijeriya za su iya yin aiki, don samun kwanciyar hankali da wadata a nan gaba.
Lokaci ya yi, da za a binciki abubuwan da ke cikin shafukan sada zumunta da kuma masu amfani da su, don ɓata sunan wasu. Sabuwar dokar aikata laifuka ta yanar gizo, mataki ne a kan hanyar da ta dace. Wannan doka, za ta taimaka wajen kare mutuncin mutane daga masu ɓata musu suna, kuma zata tabbatar da cewa an yi amfani da kafofin watsa labarai cikin gaskiya.
Sanata Shehu Buba Umar fitaccen misali ne, wanda ba ya siyasar yaudara da ɓatanci. Waɗanda ke sukan sa, da ɓata masa suna wataƙila suna faɗin Haka ne don ya kayar da su a siyasa, ko kuma suna ƙoƙarin samun karɓuwa ta hanyar ɓata wa wasu suna. Sai dai ƙoƙarin nasu, ba zai yi nasara ba, domin har yanzu mutuncin Sanata Buba yana nan.
Yana da matuƙar muhimmanci a gurfanar da waɗanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kotu, kuma doka ta ɗauki matakinta. Da wannan sabuwar doka da aka kafa, a wannan zamani da muke ciki ana amfani da hanyoyin fasaha na AI‚ wajen haɗa hoto ko bidiyo domin biyan wata buƙata, don haka ba komai ne aka gani a yanar gizo za a aminta da shi ba.
Saboda ɗaukakar da Sanata Shehu Buba Umar ya samu, ya kasance yana tare da masu bata masa suna ta hanyar yaɗa labaran ƙarya a kansa, amma jajircewarsa wajen yi wa jama’a hidima da taimakon da yake yi, sun sa ya yi suna a matsayin shugaba mai ƙwazo da sadaukarwa. Naɗin da aka yi masa a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin tsaro da leƙen asiri, wata shaida ce ta ƙwarewa da gogewarsa.
Haka kuma hanyoyin da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ke bi, wajen magance matsalar tsaro, wanda ke ba da fifiko wajen tattaunawa, da cuɗanya da al’umma, da cigaban tattalin arziƙi, ya tabbatar da alƙawarin da ya ɗauka na magance matsalolin rashin tsaro a ƙasar nan.
Wannan hanya ta gano cewa ƙalubalen tsaro galibi alamu ne na batutuwa masu zurfi kamar talauci, da rashin daidaito. Ta hanyar tattaunawa zai iya taimakawa wajen haifar da ingantaccen yanayi da kwanciyar hankali.
A taƙaice, Sanata Shehu Buba Umar yana fuskantar waɗannan zarge-zarge na ɓatanci ne kawai saboda yadda tauraron sa ke haskawa musamman ganin yadda kiraye-kiraye ke ƙara yawa akan ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Bauchi a shekara dubu biyu da ashirin da bakwai.
Daga karshe, ina fatan wannan rubutu ya ƙara bayyanawa ƙarara yadda wasu ɓatagari ke sukar sa musamman ma a kafofin sadarwar zamani da wasu gidajen jaridun ƙasar nan. Amma yanzu tunda aka rattaɓa hannu akan dokar ɓatanci a yanar gizo wato cybercrime, waɗanda ke irin wannan za su shiga hannu kuma a tuhume su, a musu hukunci daidai da abinda doka da tanadar.
Mustapha Abubakar, ya rubuto wannan sharhi ne daga Jihar Kano.
Comments
Post a Comment