2027: Hon. Dalhatu Shine zabin Al'umma

Siyasa wata abace dake baiwa al'umma yancin fadin albarkacin bakinsu musamman akan abinda ya shafi lamarin gudanar da mulki wanda hakan ya shafi rayuwar su Kai saye.

Hon Muhammad Dalhatu nagarcaccen cikakken dan kasa mazaunin magama Gumau wanda kuwa ba lallai sai kana zaune dindin din a gari kake zama dan gari ba.  Ga misali Hon. Haruna Tilde sohon dan majalisan tarraiyya mai wakiltan Toro a kano yake da zama amma bai canja shi a matsayin dan Tilde ba. 

Wannan matashi ne mai son cigaban matasa da taimakawa al'umma ba tare da cin fuskan su a kafar sada zumunta soshal midiya ba.  A zaman sa hadimin Senator Shehu Buba Umar, mutane da dama sun anfana.

Hakan tasa al'umma masu kishin Toro/Jama'a ke kira yazo ya wakilce su a matsayin dan majalisa mai wakiltan yankin a zaben 2027 dake tafe. Mutane musamman mata da matasa nada yakinin cewa Hon. Dalhatu zai kawo sauye sauye na cigaba a fadin Toro/Jama'a da yardan Allah. 

Naga wasu suna yawo da farfaganda cewa shi ba dan Toro bane wanda hakan ni bai bani mamaki ma duba da cewa a baya tun 1999 tsohon Gomna Adamu Mu'azu ya fuskanci wannan siyasar bakonta a matsayinsa na bafullace.  Daga baya Mallam Isa Yuguda shima aka jefe shi cewa dan kamaru ne wasu suce dan Jos ne.  Haka Senator Shehu Buba Umar da Hon.  Ismail Haruna Dabo duk sun fuskanci wannan siyasar kabilanci amma suna mulki.  

Kirana shine, ya kamata mu guji irin wannan siyasar cin fuskan da cin mutunci da bazai haifar mana da komai.  Cancantar sa ne kawai ganin cewa yan adawa hankalin su ta tashi bisa karbuwan da wannan bawan Allah yayi cikin kankanin lokaci.



Hon Muhammad Dalhatu yana da manufofi masu  Kyau musamman wajen samar da ayyukan da sana'o'i 
da kuma kokarin inganta kiwon lafiya ,noma da 
samarda ababen more rayuwa da kuma ayyukan raya karkara. Wadannan sune kadan daga manufofin sa dasu daya. A yanzu baya kan kujera al'umma sun shaida balle idan ya samu dama Wakilci. 


Ina tabbacin cewa mutane sun dau harami kuma sun daddara daga tsohon zanje game asalin sa domin kuwa anyi abaya bata cimma ruwa. A yanzu yana da kyau mu gane cewa al'umma ansha su kuma sun warke.  

Comments

Popular posts from this blog

Prof. Yauta Under Fire: NANS Demands Reversal of Gombe University Fee Increment

DRUG SHORTAGE CRISIS: NYCN DEMANDS ACCOUNTABILITY FROM FTH GOMBE

Dr. Agunloye's Signature Discrepancies Raise Concerns