Medical Career Academy Jos ta Kaddamar da Kwakwasan Degiri don inganta kiwon lafiya.

Daga: Abdulkadir Mohammed

Makarantar kiwon lafiya Mai Zaman Kanta, Medical Career Academy dake garin Jos,Babbar birnin Jihar Filato,na dab da Kaddamar da Kwakwasan digiri domin inganta kiwon lafiya a fadin jihar da kasa baki daya.

Babban diraktan Makaranta dake garin Jos Hajiya Fatima Usman ce bayyana haka a wani hiranta da manema labarai a offishin ta dake harabar Makarantar dake Jos.

Tace Kaddamar da Kwakwasan zai Kara fadada da kuma baiwa masa dama don cike guraben karatu a fadin Kasar nan duba karuwan yawan dalibai masu neman guraben karatu a najeriya.

Kwakwasan da aka Kaddamar sun hada da digiri a Public Health Nursing,Basic Public Education, Nutritional Health Education,Community Health Education da Nursing Health Education Professional.

Akwai School Health Education, Emergency Nursing da Community Health Wanda duka suna da inganttacen rigista da Gomnatin jiha da kuma hukumomin Gomnatin taraiya. 

Ta bayyana Farin cikin ta bisa yanda Al’umman Kasarnan musamman yankin Arewa Suka ke hubbasa wajen kawo Yayan su a Wannan Makaranta ta Medical Career Academy Jos.

Amma tayi kira ga iyayen yara dasu Kara kokari wanen biyan kudin kudaden Makaranta domin daga wannan ake biyan alawus Malamai masu gabatar da inganttacen karatu a kowani fannin lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Prof. Yauta Under Fire: NANS Demands Reversal of Gombe University Fee Increment

DRUG SHORTAGE CRISIS: NYCN DEMANDS ACCOUNTABILITY FROM FTH GOMBE

Dr. Agunloye's Signature Discrepancies Raise Concerns