Garin Jos ta Cika Makil da Masu Sarautun Gargajiya yayin Bukin Yaye Daliban Medical Career Academy, Jos.

Daga: Munnir Shuaibu


Makarantar kiwon lafiya Mai Zaman Kanta, Medical Career Academy dake garin Jos,Babbar birnin Jihar Filato, ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na farko Wanda aka gudanar ranan Asabar Shida ga watan Mayu shekera dubu da ashirin da uku.

Yayin yaye daliban,an yaye dalibai da dama a bangaren Public Health da suka kammala karatu a wannan makaranta, tare da rantsar da sababbin dalibai guda 90, da aka dauka.

Da yake gabatar da jawabi a wajen bukin yaye daliban,Mai girma Sarkin garin Bura dake karamar Hukumar Ningi,Jihar Bauchi, Alhaji Ya’u Shehu ya yaba wa wannan makaranta kan koarin da ta ke yi wajen yada ilimi a fadin Kasarnan.

Ya ce hanyan da kawai za’a kawo ci gaba a kasa, shine baiwa Al’umma ilimi musamman Yaya Mata Wanda ilimantar da mace daya tilo kamar illimartar da Al’umma ne gaba daya.Babu abin da zai kawo mana cigaba da zaman lafiya a kasar nan, kamar rungumar harkokin ilimi.

Da yake tasa Jawabin,Manajan Daraktan wannan makaranta, Dokta Rabi’u Ahmed, ya bayyana cewa an bude wannan makaranta da Hedkwatarta dake garin Kaduna ne, don horar da dalibai kan fannonin kiwon lafiya daban-daban.Ya Kara da cewa,wannan makaranta, tana daya daga cikin fitattun makarantun kiwon lafiya a kasar nan.

YaCi gaba da cewa, Wannan makaranta tana da rassa a Jihohin Taraba da Yola da Kano. Kuma muna da burin ganin mun bude, rassan wannan makaranta a dukkan Jihohin Najeriya.Ya musunta rade-raden da wasu bata gari kiyi game da wannan Makaranta cewa bata da register da Hukumo mi.

Muna tabbatar da cewa Wannan labarin kanzo kurege ne Wanda makiya Suke yadawa ,Amma yau sun ji kunya a idon duniya da Wannan bukin yaye daliban da mukayi. Muna Kara tabbatar muku da cewa Wannan Makaranta nada cikakken lasisi daga hukumomi na gomnati wanda keda hakkin kula da Makarantun kiwon Lafiya a fadin Kasarnan. Kuma Nan bada jimawa zamu fara gabatar da kosasai digiri a fannoni daban daban domin kuwa Muna daf da kaddamar da medical University.

Tun da farko a nata jawabin, Shugaban wannan makaranta a shiyar Jos, Hajiya Fatima Usman ta bayyana cewa an bude wannan makaranta a garin na Jos ne,a shekara ta dubu da Sha takwas.Acewar ta, sun yaye dalibai guda 20 ne da suka kammala makarantar, a yayin da aka rantsar da sababbin dalibai guda 90 da aka dauka.

Hajiya Fatima ta bayyana Farin ciki ta bisa yanda Al’umman Kasarnan musamman yankin Arewa Suka Yi hubbasa wajen kawo Yayan su a Wannan Makaranta ta Medical Career Academy Jos.Ta tabbatar wa iyaye da cewa wannan Makaranta nada korarrun Malamai a kowane fanni don bada ilimi ingantacce wa dalibai.

Ta kara da Cewa,Ta ce “wadannan dalibai da aka yaye, akwai wadanda suke zo daga Jihohin Bauchi da Gombe, Nasarawa da Taraba da kuma garin Abuja.A cikin sababbin dalibai guda 90 da muka dauka, guda 40 marayu ne da wani mai hali ne ya dauka nauyin karatunsu, domin muna daukar marayu a wannan makaranta.

Manyan baki Suka halarci Taron sun hada Hakimin Kasar Toro Kuma Katukan Bauchi, Hakimin Kasar Duguri Y. M Baba,Sarkin Bura ,Mataimakin Commissioner Yan Sanda na Birnin tarayya,Abuja.Yan Siyasa,Yan Jaridu daga gidan talabijin na kasa Wato NTA,PRTV,Kanfanin Jaridu da Suka hada da Daily trust, Blueprint, Gaskiya tafi Kwabo da iyayen dalibai da Kuma Malaman addini.

Comments

Popular posts from this blog

Prof. Yauta Under Fire: NANS Demands Reversal of Gombe University Fee Increment

Dr. Agunloye's Signature Discrepancies Raise Concerns

Gombe Rep, Ali Isa, Urged to Drop Case Against Thomas Umar