SIYASAR TORO: HASKEN ZAMANI NE MAFITA A 2023.Daga: Sani Danaudi Mohammed
Kamar yadda kundin sarrafa bayanai na yanar gizo wato Wikipedia ya bayyana Ƙaramar Hukumar Toro da ke Jihar Bauchi a Tarayyar Nijeriya itace ƙaramar hukumar da ta fi kowacce girma a faɗin Nijeriya, ko ma dai a ce yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya. Mazaunin Hedkwatar ƙaramar hukumar Toro na yanzu ya tattaro wasu muhimman abubuwa da suka shafi batun da wannan rubutun nawa ya ke son yin nazari a kansu. Amma kafin in fara warware zare da abawar, bari mu ɗan yi waiwaye dangane da matsayin ita kanta Nijeriya, wanda a wani ɗan yanki nata ne ƙasar Toro ta ke. Wannan zai iya zama mana ɗan ba, don a fahimci bayanan dalla dalla.
Karamar hukumar Toro dukda yanda Allah ya albarkace ta da manya manya mutane wanda ke rike da madafun iko kama daga jaha harma kasa baki daya.Amma rashin ci gaba musamman rashin aiki yi ya mana katutu musamman cikin matasa. Wannan ne yasa matasa suka tashi saye wajen ganin cewa sun kawo sauyi na gari domin canja siyasar yankin a zaben gama gari mai zuwa.
Sanannen abu ne kasancewar Karamar nada yawan ƙabilu.Lura da irin waɗannan bambance-bambance,lallai abu ne mai matuƙar wuya tafiyar da su a dunƙule guri guda.Amma ya zama tilas ,mu manta da wadannan banbamcen wanda sune silan domuwowin dake fustan yankin yanzu.kasancen cewar Karamar hukumar na daya cikin wasu kananan hukumomin Najeriya dake fidda dan majalisan tarraya. ya zama wajibi mu bude kunnuwa kada mu bari yan kwanton bauna su kara jifa mu cikin halin ni yasu a Shekaru hudu masu zuwa.
Amfani da hikima a wa’azin gyara kayanka
Tun bayan da Nijeriya ta koma tubar dimukraɗiyya a shekeran 1999, gwamnatocin baya da aka yi sun yi ta ƙoƙarin ganin sun haɗe kan al’ummar ƙasar a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya. Sai dai cimma nasara wajen tabbatar da wanzuwar taken ƙasar na, haɗin kan mabambantan jama’a, ya zama tamkar mafarki a yanayin da ƙasar ke ciki, da kuma yadda al’ummar ƙasar suke kallon junan su.Wadannan Mummunan dabiu suke ci mana tuwo a kwarya a Karamar hukumar Toro dukda daman muke dashi wajen kawo sauyi na gari.
Nuna bambance bambancen addini da ƙabilanci da ya yi yawa a ƙasar ya mayar da ƙasar wajen da shugabanci ya ke da wuyar sha’ani. Yanzu haka a yanayin da mafi akasarin jihohin Nijeriya ke ciki, nazari kan sasanta rikice-rikice ya wuci batun wani Kwas da mutum zai je jami’a ya karanta don a ba shi shaidar kammalawa. Da dama daga cikin Gwamnonin ƙasar nan, yau da gobe ta sa sun zama masana warware saɓani da rikice-rikice a jihohin su, sakamakon irin yadda faɗace-faɗace masu nasaba da addini da ƙabilanci suka yi yawa a jihohin nasu.
Wannan hali da ake ciki ne ya haifar da yanayin siyasar da yanzu ake gani a ƙasar, siyasar addini da ƙabilanci. Ya zama dole a faɗi gaskiya, wannan mummunan yanayi ya haifar wa qasar koma baya mai yawa. Shi ya sa dole a ja hankalin matasan ’yan siyasa masu tasowa su fahimci irin haɗarin da ke fuskanto su, a matsayin su na manyan gobe, domin samar wa ƙasar makoma tagari.
Allah ya albarkaci yankin Toro da wasu tsayayyun matasa,Masu kima da kuma gaskiya da rikon amana da sayin daka wajen kawo sauyi na gari musamman wajen ganin matasa da mata iyaye sun samu dogaro na kansu. Hon. Ismael Dabo Haruna ( Talban Toro ) wanda ake wa lakabi da Hasken Zamani na gaba gaba wajen ganin Al''umma Karamar hukumar Toro sun anfana daga dunbin alherai dake tattare da kujeran Majalisan wakilai na tarraya.
Marigayi Maitama Sule (Ɗan Masanin Kano) ya taɓa faɗin cewa, mulki na iya zama ne kaɗai a hannun shugaba nagari mai adalci. Shugaba da jama’a suke jin daɗinsa shi ne wanda ba ya nuna musu wariya, kuma ba ya bambanta wani sashi na jama’ar sa a kan wani sashi, ya ɗauki kowa daidai da kowa. Wannan hazikin matashi Yayi tsayuwar daka,don ganin irin wannan gurɓatacciyar siyasar da nuna bambancin bai samu wurin zama a yankin ba. Hasalima ,bayan yayi takara kujeran dan Majalisan Jaha (Toro/Jama'a) a 2015,Yayi takaran kujeran Majalisan tarayya na Karamar hukumar Toro lokacin cike gurbi a 2018,Ya sake takara a 2019 na kujeran Majalisan tarayya kafin Ubangiji Allah ya bashi nasara a karkashin inuwar jami'ar APC mai mulki don yi mata takara a zabe mai zuwa.
Babban matsalolin dake fuskan tan mu a halin Yanzu daga wadanda muke turuwa su mana wakilci shine,Rashin nuna adalci da gaskiya wajen tafiyar da sha’anin mulki, shi ya ke sa jama’a kukan an zalunce su ko an danne musu wasu haƙƙoƙin su.Wannan rashin adalci da'aka dade ana yiwa Al''umma Karamar hukumar Toro ya sanya HARKEN ZAMANIN shiga zuciyan Mutane a kankanin lokaci.Shi a kullum mutum ne wanda ke kokarin ganin an kawo sauyi na gari domin ganin an taimake Al''umma sabanin yanda wasu suka kasa bambanta sha'anin mulki,hakkin Jama'a da kuma tara dukiya da baitilmalin Gomnati.
Talba yana daga cikin matasa na Wannan yankin wanda hatta wasu abokan hamaiyar sa na siyasa sun bada shaida halin sa wajen gaskiya da rikon amana.Ashe kuwa ,ƙaramar hukumar Toro da sauran yankuna zasuyi alfa''hari da wannan dan halak wanda duniya ta shede shi da halin dattaku. Wannan shi zaisa, rabe raben tsarin tafiyar da harkokin al’umma da ya haɗa da ɓangaren Gomnati ya isa ga Al''umma a matsayin romon dimokoradiya.
Wani abin ban sha’awa da ɗaukar hankali shi ne yadda wannan matashi ke anfani da daman sa wajen inganta rayuwar Al''umma musamman matasa da mata wanda sune ginshikin cigaban kowane yanki. Anyi kididdigan cewa,Kimanin Mutane sama da 500 ke anfana daga Kanfanin sa na HAFDALA kama daga nan gida Toro da waje. Wannan kadai ya ishe mu tunani wajen fahimtan manufar sa ga Al''umman Toro idan Ubangiji Allah ya bashi nasara a zabe mai zuwa.A Kwanakin baya ,ya kaddamar da HASKE KUDIN JARI ga mata masu kananan masana'antu.Irin wadannan sarinne ke bamu karfin guiwa cewa idan ya zama dan Majalisan tarrayya mai Wakillitan Karamar hukumar Toro to lallai abunda muke karantawa a jaridu zai zo mana yankin mu.
A halin da kasar nan ke ciki,aiki ya zama na yan Majalison dokoki dana tarraya wanda dole sai kuna shugaba na gari zaku ji kamshin wannan labari.Dayawan wasu daga cikin su sayarwa suke maimakon rabawa talakawan da suke wakilta.Muna ji muna ganin yadda wakilai irinsu Sanata Aisha Dahiru Binani suke rabon dubban buhuhunan takin Zamani wa manoma da sauran su. Kamata mu fahimci cewa mutane irin su Talba suna da gogewa matuka dasu iya shiga su fita domin ganin cewa Karamar hukumar Toro ta anfana da duk wani sari da Gomnati zata kawo.
Ganin Wannan ƙoƙari da ya ke yi babu shakka shi zai ƙara nunar masa da yiwuwar samun cigaba da goyon bayan jama’ar yankin a babban zaɓe mai zuwa na 2023. Kuma kasancewar sa matashi wannan abin da ya ke yi zai taimaka masa wajen samun damar cigaba da wakilcin na gari idan ya tafi Majalisar Wakilai ta Tarayya.Yazama wani tauraro ne da ake alfahari da shi. Sannan ana yi masa ganin ƙwararren da idan ya samu wannan damar zai iya kawo sauyi a siyasar Toro. An yi la’akari da haka ne ganin irin yadda ya ke tafiyar da siyasar sa ba tare da nuna wani bambanci ko wariyar wani ɓangare ba.
A matsayina na mai kishin samar da shugabanci nagari a ko’ina a Nijeriya.Akashin gaskiya,Lokaci ya yi da za a kawo canji a siyasar Toro. Gaskiyar magana shi ne ya kamata a samar da wani jajirtacce da zai kawo sauyi da cigaban da zai yi tasiri wajen inganta makomar siyasar Toro da zamantakewar al’ummarta ba tare da kallon addini ko wata ƙabila ba. Ya kamata a ba da goyon baya ga mutumin da aka tabbatar da ingancin sa da ƙwarewar sa wajen ganin ya samar wa ƙaramar hukumar Toro shugabanci nagari da cin moriyar dimukraɗiyya.
A taƙaice, bayanan da na yi ta ginawa a baya na yi su ne domin nuna bayyana irin ƙwararan dalilan da na ke da su, waɗanda kuma na ke ganin za su amfani ƙaramar hukumar Toro wajen samun wakilci nagari, shugabanci mai adalci da kuma uwa uba zaman lafiya mai ɗorewa.duk wasu da za su yi ƙoƙarin kawo wa al’ummar Toro wani mugun ra’ayi da zai ruguza kyakkyawan tarihin da suke da shi tun iyaye da kakanni na son juna da haɗin kai su kiyayi kansu daga wannan mugun tafarkin da suke shirin jefa kansu.Masu hikimar magana dai na cewa, idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, sai ka shafa wa na ka ruwa. Aiki da hankali, ya fi aiki da agogo.
Wannan dalilan yasa muke kwarin guiwa cewa idan an bashi dama zai kawo sauyi na gari kuma zai zamo ma Karamar hukumar Toro Mafita Insha'Allah.
Comments
Post a Comment