Nastura Sheriff Yayi Ganawan Sirri da Bello Yabo a Sokoto.
Daga: Abdullahi Ahmed
Shugaban amintattun Gamaiyan Kungiyoyin Arewa wato CNG (Dr) Nastura Ashir Sheriff ya ziyarci Jihar Sokoto yau Lahadi domin jajantawa iyalan wadanda barayin daji suka musu kisan gilla a makon data gabata.
Shugaban yayi anfani da wannan daman ya ziyarci shahararren Malamin addinin Musuluncin nan wato Bello Yabo inda sukayi tattataunawan sirri wanda kawo yanzo babu Wanda zai iya fadin hakikanin Gaskiya abunda tattaunawan tasu ta kunsa.
Mutane da dama na sharhi la'akari da matsalolin da data addabi yankin Arewa kama daga matsalan tsaro da kudirin Gomnatin tarraiya na cire tallafin man fetur a shekara mai zuwa.
Sayuwan dakan da Wadannan bayin Allah keyi akan abunda ya shafi Al'umma musamman Talakawa a Arewancin Najeriya ya sanya mutane ke ganin ganawan tasu baiwuce kaman ta kullum ba.
(Dr) Nastura Ashir Sherrif yayi anfani da wannan daman domin yin addu'oi ga Wadanda suka rasa rayukan su da Kuma Samun zaman Lafiya Mai dorewa a Arewa masu yamma da Kasa baki daya.
Daga karshe, Yayi kira da Babban murya ga Gomnatin tarraiya dana Jihohi dasu yi kokari wajen tabbatar da kare rayukan Al'umma da Kuma dukiyoyin su.
Comments
Post a Comment