MATSALAR RASHIN TSARO MATSALAR AREWA CE BA NAJERIYA BA: Dikko Muhammad
Najeriya ba qasa daya ba ce. Qasashe ne da yawa aka hada a takarda. Wannan ya sanya matsalar tsaro ba ta samun wuri a jaridu na kudancin qasar.
Abun da ya kamata mu yi shi ne, gwamnonin Arewa su zauna da manyan mutane (Sarakuna, Malaman addini, 'Yan kasuwa, 'Yan boko, Ma'aikatan tsaro, da sauransu) domin tattaunawa ta gaskiya akan matsalar nan. Ya zama dole mu rage tunanin samun warwarewar matsalar nan daga Abuja. Yin hakan 6acin rai da rarrabuwar kai kawai zai cigaba da kawo mana.
Akwai wata karin magana a harshen yarbanci da za'a iya fassarawa kamar haka, "Fulani ya kashe Bahaushe; ina ruwa na?" Wannan shi ne zahirin yadda su ke kallon matsalar. Wannan ya sanya idan ka ji sun ambaci Boko Haram to zagin mu zasu yi.
Ya kamata Arewa ta rage dogaro da Abuja ta fara neman hanyoyin da zata rayu da kanta tun daga kasuwanci zuwa tattalin arziki zuwa ilimi da sauransu. Kai har harkar Shari'a ya kamata a yi ma ta gyaran da zai tafi da tunani da kuma haqiqanin rayuwar mutanen Arewa.
Mafi akasarin mutanen Arewa sun hadu a addini da al'ada da kuma harshe. Amma kowace jiha sai ta ce zata warware matsala ita kadai. Wannan ya sanya idan an warware matsala a Zamfara, sai ta koma Sokoto ko Katsina ko Jigawa. Amma idan aka fuskanci matsalar ta mahangar Yankin Arewa gaba daya, to inshaAllah an gama warware ta ko ina a yankin.
Comments
Post a Comment