DALUNG YA TABBATA GARKUWAN TALAKAWAN AREWA ( KASHI NA 1): ZANNA A.

Najeriya na daga cikin kasashen duniya wanda keda yawan kabilu a duniya . A halin da ake ciki Najeriya ce ta uku a kasashe dake da yawan kabilu bayan kasar papua New Gunea da Kuma Kasar Indonesia dake lardin larabawa. An alakanta rashin cigaba da Kasar Najeriya ke fama da ita musamman a yankin Arewa da bambance-bambacen yare da adini wanda shugabanni sukayi nasaran cusa wa al'umman su don biyan bukatun su na Siyasa Wanda har hanzu keda matukan tasiri a zukatan al'umma Najeriya musumman lokutan zabe na gama gari. 

Shugabannin Najeriya na karnin farko kamar su Marigayi Sardauna, Tafawa Balewa da Awolowo sunyi mulkin su ba tare da nuna bambancin addini ko yare ba Wanda hakan shiya basu nasaran zamowa zakarun gwajin dafi Wanda har hanzu ake alfahari dasu . Tun bayan rasuwan wadannan bayin Allah kimanin shekaru hamsin da hudu( 54) Najeriya ta kasa gano inda gizo ke saka sabida wasi da al'adun mu Wanda iyaye da kakanni suka daura mu akai. Al'ada turbace babba Wanda keda matukan tasiri wajen kawo kekkyawan zamanta kewa sakanin dumbin yaruka da Kuma mabiya addinin Musulunci dana kirista.

Tun dowowan mulkin dimokoradiyya a shekara alif dari tara da casa'in tara Najeriya ta since kanta acikin mummunan akidu na nuna bambancin addini ko yare Wanda har hanzu ke cigaba da kawo koma baya a horkokin gudanar da kasa . Hakika Arewa tayi babban rashin mutane irin su Sardauna Wanda sunyi sayuwan daka domin kawo sauyi da cigaba mai daurewa a Arewancin Kasarnan Wanda cike gurbin su keda matukan tasiri duba da halin da Arewa ta tsinci kanta a ciki na kashe- kashen mayakan Boko Haram,sata mutane don biyan kudin Fansa,rikicin manoma da makiyaya ,masu sace shanu da sauran su. Tarihi ya nuna cewa a shekarun baya duk inda kaga kabilun arewa tare suke da bafulatani wanda wannan na nema Zama tarihi .

Abunda yasa na dauki wannan takaitaccen tarihin badon komai ba saidai na nuna muhimmancin da mutane irin su tsohon ministan wasanni da matasa Barista Solomon Dalung keda shi matukan anason dawowa da martaban Arewa a matsayin tsinsiya daya madauri diya .Akashin gaskiya bansan Dalung ba Kuma bantaba ganinsa ba Kuma har wayau bansan inda zan ganshi ba amma sayin dakan da yayi lokacin da tsohon Shugaban kasa Jonathan yake mulki lokacin duk Yan Arewa basu da baki yasa na dauke shi tamkar mutane dake da hali irin  nasu Marigayi Sardauna. Yana da hali Wanda kadan ne daga cikin mutanen Najeriya keda ita wajen fyede gaskiya komai dacin ta . Jajircewan sa akan abubuwa da suka addabi yankin nan yasa da yawa mutanen jihohin Arewa ke alfahari dashi akoda yaushe domin samun Mutum irinsu a halin da ake ciki sai anyi da gaske .

Yankin Arewa nada gaba gaba a tarihin yawan wadanda suka mulki Najeriya daga lokacin mulkin Soja zuwa farar hula amma ahalin da'ake ciki yankin yafi kowane daga cikin yankunan da muke dasu a Najeriya fama da muggun talauci, rashin aikin yi, tsaro da fyade da sauran su. Abun takaici anan shine samun Mutum guda dazai yi sayin daka wajen tabatar da cewa an tunatar da gomnati musamman gomnonin Arewa akan abunda ya kamata suyi ya gagara . Barista Solomon ya zamo Mutum guda tilo Wanda fyade gaskiyar sa ya jawo masa mosoya daga kowonne lungu da tsako na Kasarnan musamman a yankin Arewa inda da yawan mutanen yankin sun dauke a matsayin garkuwa bisa tausin zuciya da yake da ita wajen Kare hakkin talaka a Najeriya. A lokacin da Arewa take cikin halin ni ya'su kowan yasan irin Makaman Yakin baka da Dalung ya jagoranta a kafafen yada labarai Wanda hakan yayi tasiri sosai wajen kifar da gomnatin PDP da Shugaba Goodluck Jonathan.

Kungiyoyin matasa a yankin Arewa da kudu suna alfahari da kasancewar sa matsayin ministan wasanni da matasa a farkon wa'adin mulkin Shugaba Buhari ba don komai ba saidon ganin cewa daya daga cikin mutanen dake dabi'a da halayen kirki irin nasa sun samu damar kawo sauyi acikin gomnatin chanji Wanda talakawan Najeriya kesa rai samun ingantaccen ruwan sha ,hanyoyi ,asibiti da wutan lantarki da Kuma tsaro . A dan karamin lokaci da yasamu ya kawo gagaruman sauyi a harkan kwallon Kafa a Najeriya amma tir gashi yanayin tirkaniyan siyasan Najeriya ta sanya shi gaza dowo wa wa'adi na biyu ko shike Ubangiji Allah yafi mu sanin dalilin da yasa hakan amma akasarin mutane a. Kullum suna cewa ai fyade gaskiyar sa ta jawo masa . Dalung a kullum ya zabi ya kunya anan duniya daya ji kunya a lahira shiyasa yake da dumbin mosoya daga cikin akasarin talakawan Najeriya yayin Kuma yake da dumbin makiya acikin al'umma dake da hanu da shuni ko Masu rike da madafun iko .

Ya zamo daya daga miliyoyin mutane baya la'akari  da yare,bangaranci, kabilanci ko addini na yan Najeriya wajen bambanta su shine kullum yana saye akan kafafun sa daram wajen ganin cewa kowan anyi masa adalci a matsayin na dan kasa ba amatsayin Mai yare ko addini ba. Ire-iren wadanan kyawawan halayen sa ya Sanya mutane da yawa keyi masa ikarin cewa shine Mutum ne Mai fuska daya wato Solomon a pilato Kuma Suleimanu a Sokoto. Abun nufi anan shine bai bambanta mutumin Jihar sa ta pilato da mutumin Sokoto Wanda Wannan shine turban hadin Kai da Marigayi Sardauna ya mutu ya bar yankin Arewa akai .

Lallai ta tabbata cewa Dalung ya zamo Jagora na gari Kuma Garkuwan talakawan Arewa domin bayan shi bamu da Wanda ke fitowa ya fada wa gomnati gaskiya game da halin da muke ciki . A lokacin da ake koremu a garuwan mu lokacin gomnatin data gabata saboda yadda aka bar Yan ta'adda suka ci karensu ba babbaka Dalung ya bada rayuwar sa da lokacin sa don kwato Arewa maso gabas da Arewa baki daya daga hanun azzalumai . A matsayina na matashi Mai son kawo sauyi a harkokin matasa da kuma al'amuran yau da kullum Ina Mai alfahari da Kuma Martaba Solomon Dalung a matsayin halattaccen da Kuma Garkuwan talakawan Arewancin Najeriya . Muna San ran irin gwaggwamayar da mukayi wajen kawo mulkin chanji ta Shugaba Buhari akan karagar mulkin cewa mutanen irinsu Garkuwan talakawan Arewancin Najeriya zasu zamanto na kusa dashi domin fada Masa gaskiya don kawo sauyi da talakan Najeriya ke sambani . Duk shike yayi kokarin kawo sauye sauye a harkan kwallon Kafa a Najeriya musumman ma wajen yaki da cin hanci ya fuskanci tirjiya Wanda hakan yayi sadanin kawar dashi a wa'adi na biyu . Hakan ya Sanya shi Zama cikakken da Wanda halinsa ke tafiya dana su Marigayi Sardauna wajen sayawa akan gaskiya koda kuwa zaiyi sanadin rayuwar ka .Wannan shine halaiyar da Kuma kadan daga cikin dabiun tsohon ministan wasanni da matasa Kuma Garkuwan talakawan Arewancin Najeriya wato Solomon Dalung.

. Zanna Abubakar momba a kungiyar Arewa youths advocate for change initiatives ( AYACI) ya rubuto daga Jihar Yobe a Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Prof. Yauta Under Fire: NANS Demands Reversal of Gombe University Fee Increment

DRUG SHORTAGE CRISIS: NYCN DEMANDS ACCOUNTABILITY FROM FTH GOMBE

Dr. Agunloye's Signature Discrepancies Raise Concerns